Saboda amfanin da wadannan wayoyin ke yi da data ne ya sanya
aka basu damar cewa, da zarar mutum ya kunna data, to su ci gaba da yin wasu
muhimman aiyuka ba tare da sun sanar da mai wayar ba (wato background data). Wasu wayoyin kuma application din su ne ke yin update
lokaci zuwa lokaci domin inganta ko kuma sabinta yanayin yanda wayar ke aiki.
Wani lokacin kuma, applications din da mutum ke yin installing a cikin wayar ne
ke amfani da wannan damar domin yin wasu ayyukan da ke bukatar data ba tare da
sun nemi izinin mai wayar ba.
Shin ko kana cikin wadanda ke fama da irin wannan matsala ta
shan data? To kwantar da hankalinka, ga hanyoyin da zaka bi domin ragewa ko
kuma tsaida wannan shan data da wayarka take yi.
Background
Data
App background data
shine babban abin da ke sanyawa waya ta rika shan data babu gaira babu dalili!
Duk da cewa wayoyi da yawa na zuwa da wannan tsarin, wayoyin android sun fi
kaurin suna akan wannan matsala. To sai dai, duk da haka, wayoyin android din
suna bada dama ga mutum domin ya zabi
applications din da yake bukatar ya rika amfani da data a ko da wane lokaci,
tare da kuma kange wasu application din daga yin amfani da data ba tare da
saninshi ba.
Domin gane ko wane application ne yake shan data ba tare da
saninka ba, to sai ka shiga cikin Settings
na wayarka, ka duba daga kasa kadan, zaka ga inda aka sanya Data Usage. Idan ka shiga wurin zaka ga
list na duk application da ke amfani da datarka, idan kaga akwai wani wanda
baka yarda da shima to zaka iya hanashi yin amfani da data har sai ya samu
izininka. Domin tsaida application daga shan data kai tsaye, sai a bi wadanna
matakan:
1 . Shiga cikin settings
2 . Duba daga kasa
kadan, akwai inda aka sanya Data Usage
3 . Idan ka shiga Data
usage, zaka ga list na applications din da ke shan data da kuma yawan datar
da suka sha
4 . Domin tsaida application daga shan data, sai ka taba
application din, wani page zaya bude.
5 . Sai ka duba daga kasa, akwai inda aka sanya Restrict app background data, sai ka taba
ko kuma ka kunna.
Haka zaka yi ma duk wani application da kake bukatar takaita
yanayin shan datar da yake a wayarka. Daukar wadannan matakan kadai, zaya
taimaa maga wajen rage yanayin yanda wayarka ke sha maka data sosai.
Wannan sune hanyoyi da zaka bi domin rage yawan data da
wayarka she amfani da ita ba tare da saninka ba. Da fatan kun amfana da wannan
kasida.
Comments
Post a Comment