Damar Samun Kudi a Internet

Muna farin cikin kawo muku wata sabuwar hanyar samun kudi a internet da ta shigo mai suna MonkuTalk.
MonkyTalk na daya daga cikin hanyoyin da suka fi farin jini wajen jama’a ta fannin samun kudi a internet, ba don komai ba sai don irin babbar damar da sukan baiwa mutane ta samun kudi ta hanyar bin wasu hanyoyi masu sauki.
Wadannan hanyoyi dama kuma abubuwa ne wadanda mutane suka saba yi –wato chatting. A wannan website, duk wani abu da ka san kana iya yi a facebook, to zaka iya yinshi a cikinsa kuma su biya ka.
Idan kayi comment akan rubutun wani, zasu biyaka. Idan ka yi posting na wani abu zasu biyaka. Idan kayi Like na wani post zasu biya. Idan ka tura ma wani message, zasu biya. Ko ko login kadai ma kayi a rana sai sun biya wani abu.
Shi wannan website yana bayar da kyauta points ne na zinari (wato Gold point) akan dukkanin abin da mutum yayi. Wannan Gold Point (gp) kuma, mutum zaya iya canja shi ya karbi kudi a lokacin da yake bukata.
Wani babban abin da yafi jan hankalin mutane game da wannan website shine, a duk lokacin da mutum yayi rajista (indai har ya bi ta hanyar wasu mutane da ake kira da Tycoon), to zasu bashi kyautar $10 (dala goma) dai-dai da N3600 kudin Nigeria.
Ganin haka ne muka ga ya dace mu shiga mu bude wannan account tare da zama Tycoon ta yanda zamu baku damar samun wannan $10 cikin sauki (ta hanyar amfani da account namu).
Idan kuna bukatar yin rajista, sai ku fara kula tare da sanin wadannan matakan kamar haka:
1.       Ku tabbatar kun shiga wannan website ta hanyar link din da zamu baku a nan kasa (domin hakan ne zaya sa ku can-canci samun wannan $10 din)
2.       Idan kun shiga ta wannan link, zaku ga sunan sadarwa ya bayyana a wajen.
3.       Idan kuma ba ta wannan link din kuka shiga ba, ko baku ga sunan ba, to akwai wani wajen daga kasa inda zasu tambaye ku cewa, Wani ya turo ku? Sai ku zabi Yes. Idan kuka cike, a shafi na gaba zasu tambayi lambar wanda ya turo ku, sai ku sa wannan lambar:  536282 (don samun damar mallakar wannan $10 da suke badawa).
4.       Abu na gaba shine, zasu tambaye ku garin da kuke bukatar shiga. Wannan gari shi ke nuna yawan abin da zaku iya samu a wannan shafi. Domin yawan mutane da ke cikin garin, shi ke nuna yawan abin abin da zaku iya samu. Muna shawartarku da ku zabi Jos, Plateau. Domin shine garin da ya fi mutane masu yawa a cikin wannan website.
5.       Daga nan kuma zasu tambayeku da ku zabi harshenku, a nan zaku iya zabar Hausa, ko kuma ma ko wane irin harshe kuke bukata indai akwai shi a website din.
6.       Abu na karshe da zasu bukace ku da ku yi domin kammala wannan rajistar shine, zasu bukaci da ku dora ko kuma ku yi upload na profile picture ko kuma DP naku. Ba dole sai kun sanya hotonku ba a nan, zaku iya sanya hoton wani abu daban.
Ga wannan link din da zaku iya bi domin yin rajistar: http://www.MonkyTalk.com/whzon/franMgr/postForGold.php?nlg=37&gold=536282
Domin yin tambaya ko kuma neman karin sani akan yanda zaku ci nasarar shiga wannan tsari, sai ku tunbemu a dandalinmu na WhatsApp ta wannan lambar +2347061599050 domin samun damar shiga wannan Group namu na musamman da muka bude domin nuna koyar da ku yanda zaku iya amfani da wannan babbar damar.

Zaku kum iya duba wannan videon domin karin bayani



Friday, 9 March 2018

Samun kudi Ta Hanyar Facebook WhatsApp da Instagram








Sanin kowa ne daya daga cikin abubuwan da aka fi yawan aikatawa a saman shafukan sada zumunta shine rabawa ko kuma sharing na links. Wannan link zaya iya kasancewa na wani labara ne, ko kuma na wani abu daban. Shin ko kun san cewa wannan abu da kuke yi a ko da yaushe zaka iya samun kudi ta hanyarsa?
Wannan ita ce tambayar da zamu amsa muku a cikin wannan kasida tamu ta “Damammaki A Internet” ta wannan lokaci. Za kuma mu nuna muku yanda zaku iya yin hakan.
Samun kudi ta hanyar rabawa ko kuma sharing din lin wani abu ne da ya jima ana amfani da shi. Sai dai ba duka daga cikin mutanenmu ba suka san da hakan ba. Abin da ke faruwa shine, mai-makon kawai mutum yayi sharing din link kai tsaye zuwa shafin sada zumunta, zaya fara sanya wannan link din ne cikin wani website, shi wannna website zaya matse wannan link din naka da ka sanya (wato za’a yi shrinking din link din), sai ya baka wani link na daban. Wannan link din ne zaka yi sharing a inda kake bukata.

Ta yaya ake samun kudin?

Idan suka baka wannan link din da ka saka, duk lokacin da wani ya ziyarci wannan shafin (inda labaran ko kuma bin da kayi sharin yake) to zasu nuna wata ‘yar talla da zata dauki seconds biyu zuwa ukku kafin shafin ya bude.

Ta yaya ake rajista da wannan tsari?

Domin shiga wannan tsari na samun kudi ta hanyar sharing din link, to sai ku taba wannan Address din:
Da zaran kun shiga sai ku duba daga kasa kadan akwai inda aka sanya Join Now. Sai ku taba wajen. Wannan zaya kai ku ga shafin da zaku yi rajistar. Da zaran kun kammala rajistar zasu bukace ku da ku shiga email din ku  domin tabbatar da wannan rajista da kuka yi. Da zaran kun tabbatar SHI KENAN! Kun kammala rajistar. Sai mi ya rage? Sai ku fara samun kudi daga link din da zaku rika sharing.

Ta ya ake samun kudi daga link?

Kaddara a ce akwai wani post ko kuma wata kasida da kuka ga an rubuta, kuma kuna bukatar ku yi sharing dinta, abun da zaku yi shine kamar haka:
1 . Ku kwafi (copy) link din da kuke bukatar sharing din
2 . Bayan kun kwafi link din, sai ku shiga a shafin adfly din da kuka rajista da shi, da kun shiga zaku ga wani wuri da zaku sanya address din da kuka kwafo. Bayan kun sanya address din sai ku taba inda aka sanya Shrink daga gefe.
3 . Bayan kun sanya shrink, za’a fito muku da wani sabon address. To wannan address din zaku kwafa sai kuje da dandalin sada zumunta kamar Twitter, Facebook, WhatsApp ko Instagram, sai ku sanya link din.
Domin duba yawan kudin da kuka samu a kan ko wane link da kuka yi sharing, sai ku duba daga kasan page din zaku gani.
A kula: Wasu lokuta idan aka yi sharing wannan link a Facebook suna nuna cewa ba daidai yake ba, amma zaku iya amfani da sauran kafafen kamar WhatsApp, Instagram, Twitter da dai sauransu a ko da yaushe.
Wannan ita hanyar da zaku bi domin samun kudi a kan abubuwan da kuke yi a kusan ko wane lokaci a cikin shafukan sada zumunta.

Friday, 23 February 2018

HANYOYIN DA AKE SAMUN KUDI A INTERNET



Idan baku manta ba, a cikin kasidarmu ta farko a kan “Damammaki A Internet”, mun gabatar da ku akan ire-iren damammaki a internet da zaku iya amfani da su domin samun kudi ko kuma wani abin amfani a internet. Kasida ta biyu kuma tayi muku bayani ne akan abubuwan da kuke bukatar tanada kafin fara wannan harka (shiga nan domin karantawa sadarwa.com). Kasidar baya-bayannan kuma a cikinta ne muka yi muku cikaken bayani akan yanda zaku iya cire kudin da kuka samu daga internet zuwa bank dinku na gida (shiga nan domin karantawa sadarwa.com). A cikin wannan kasidar kuma, zamu yi muku sharhi akan yanda dimbin hanyoyin da zaku iya bi domin samun wani aiki da za ku iya yi a biyaku a kan Internet.
Akwai hanyoyi da yawa da ake bi wajen samun kudi a internet. Wasu hanyoyin na bukatar sai mutum ya saka wani jari, wasu kuma basu bukata. Wasu hanyoyin na bukatar mutum ya mallaki website nashi  na kansa, wasu hanyoyin kuma basu bukatar yin hakan. Har wa yau kuma akwai wasu hanyoyin da ke bukatar amafani da computer wasu kuma basu bukata. Ga bayanin wasu daga cikin wadannan hanyoyin kamar haka:
1.    Pay Per Click (PPC)
          Pay Per Click wani tsari ne da wasu kamfanoni ke amfani da shi domin biyan masu yi musu talla a duk lokacin da wani ya ziyarci website din kamfanin ta hanyar shi wannan mutumen da ke yi musu  tallar. Domin samin kudi ta hanyar PPC, abin da mutum ke bukatar yi shine ya fara yin rajista da wannan kamfanin. Bayan mutum ya yi rajista, zasu bashi wani adreshi ko kuma link. Shi wannan adreshi (wato link) da zasu baiwa mutum shine domin ya yi  amfani da shi wajen tallata haja ko kuma website din wannan kamfani, duk lokacin da wani ya ziyarci shafin wannan kamfani ta hanyar wannan link da suka baiwa mutum, to za’a biya shi wani kaso na musamman. Wannan link da zasu baiwa mutum zai iya sanya shi a website dinshi idan yana da shi, ko kuma ma zaya iya amfani da social media (kamar Facebook, WhatsApp ko Twitter)  wajen tallata wannan website na su (wato sharing din wannan link da suka bashi).
2.   Referral
Referral , ita ce kusan hanyar da tafi ko wace hanya saukin samin kudi a internet. A wannan tsari, kamfanoni da ke bukatar mutane su san da su , ko kuma suna siyar da wasu kayayyakin amfani, sukan bada wannan irin damar ga mutane abokan huldarsu, domin yi musu talla. Kawai abin da wadannan kamfanoni ke bukata shine mutum ya nemo wani ko kuma wasu domin su yi rajista da su ta hanyar website nasu, su kuma zasu biya mutum wasu kudi na musamman. Kudin da irin wadannan kamfanoni ke bayarwa ya kusa lillinka wadanda ake samu a sauran tsaruka. Suma wadannan kamfanoni rajista ake yi da su, idan mutum na bukatar yin huldar referral da su, sai su baiwa mutum adreshi ko kuma link da za yayi amfani da shi domin gayyatar mutane ya zuwa shafinsu. Duk mutumen da ya kammalla yin rajista da wannan shafi nasu, kuma ya zamto ya yi hakan ne ta hanyar link din da suka baka, to kai kuma zasu biyaka wani abu a irin wannan tsari. 
3.    Affliate Marketing
Wannan shima wata hanyar ce da ake samun kudi a internet ta hanyar yi ma website ko kum a company tallar kayan da suke siyarwa. Wannan tsari za’a iya dangantashi da dillanci a  Hausance, domin suma zasu baka link ne domin raba ma jama’a, duk mutumin da ya sayi kayansu ta hayar wannan link din da suka baka, to za’a biya ka wani kaso daga cikin wannan ciniki da ka kawo musu.
4.    YouTube Videos
Wata hanya da ba kowa ne ya san da ita ba ko kuma ya san amfaninta ba a cikin mutanenmu shine yadda za’a iya samin kude daga YouTube. Wannan hanya ce mai matukar sauki. Kawai abin da kake bukata shine ka mallaki google account (gmail). Za ran ka mallaki gmail zaka iya zuwa YouTube domin da bude channel. A cikin wadannan channel din ne zaka rika dora bidiyoyinka. Domin samin kudi a duk lokacin da wani ya kalli wannan bidiyo sai ka tabbatar ka shiga wajen settings kayi checking ko kuma ka zabi “monetary” , wannan zaya baka damar da zaka sami kudi a duk lokacin da YouTube suka sanya talla a cikin bidiyonka.
5.   Survey
Survey ita ma wata hanya ce da mutane ke samun kudi a internet ta hanyar amsa wasu tambayoyi. Akwai wasu shafuka a internet wadanda aikinsu shine su ba wasu kamfanoni ko kuma hukumomin gwamnati damar yin bicnike ta hanyar jin ra’ayoyin al’umma. Su wadannan website suna karbar tambayoyi ne daga kamfanoni ko kuma hukumomin da suka yi yarjejeniya da su, bayan sun karbi wadannan tambayoyi, su kuma sai su tura ma mutanensu wadanda suka yi rajista da su. A duk lokacin da mutum ya amsa wannan tambaya da suka turo mashi, to zasu biya shi wani abu. Wasu website din suna baiwa mutum kudi ne kai tsaye, wasu kuma suna baiwa mutum maki ne (marks) ta yanda idan makin ya taru, to mutum zaya iya karbar kudi ta hanyarsa. Domin shiga wannan tsarin, mutum zaya nemi wadannan websites ne sai yayi rajista da su. Bayan mutum yayi rajista da su, to a duk lokacin da aka samu wannan aiki, su kuma zasu turo mashi, idan kuma ya amsa, to zasu bashi maki ko kuma kudi.
6.   Advertising/Ads (Talla)
Shima wannan wata hanya ce da ake samun kudi a internet ta hanyar yin talla. Amma wannan hanyar ta sha bamban da referral da kuma Internet Marketing, saboda shi advertising a mafi yawancin lokaci mutum yana amfani da website dinsa ne wajen sakawa ko kuma nuna tallar. A wannan tsari na Advertising (ko kuma Ads a takaice), mutum zaya sanya link, hoto ko kuma hoton link (wato image link) na wannan kamfanin. Shi wannan tsarin ya bambanta, domin mutum zaya iya yi ma wani kamfani na internet ko kuma ya samu wani kamfani ko masana’antu na wasu mutane da ya sani, sai  su yi yarjejeniya a kan zaya saka tallarsu a cikin website dinsa. Idan tallar wani website ne kuma mutum zaya saka, to yana bukatar yayi amfani da link ko kuma image link nasu, ta yanda duk wanda ya ziyarci shafin ko kuma ya kalli wannan talla, to zasu biya shi wani abu. Idan kuma wani kamfani ne mutum zaya sanya ma talla, to kawai abin da yake bukatar sanyawa shine rubutu ko kuma hoton talla na kamfanin (bayan sun yi yarjejiya akan abin da zasu biya shi).
Wadanna sune wasu daga cikin hanyoyin da aka fi amfani da su wajen samun kudi a internet, a kasidunmu na “Damammaki A Internet” da zasu biyo baya, in Allah ya so, zamu fara daukar daya bayan daya daga cikin wadannan hanyoyin tare da yin sharhi akan yanda zaku iya shigar tsarin tare da kuma amfana daga gareshi.

Friday, 16 February 2018

YANDA AKE HADA BANK ACCOUNT DA PAYPAL



Idan ba’a manta ba, a cikin kasidarmu da ta gabata mun Magana ne akan abubuwan da mutum ke bukata kafin ya fara shiga harkar samun kudi a internet (wato Making money online). A cikin waccan kasida da ta gabata mun yi tsokaci akan wadannan abubuwa wadanda suka hada da Bank account, Master card da kuma PayPal account wanda shi kuma yana matsayin kamar bank na saman internet (shiga nan domin karanta waccan kasidar ta baya sadarwa.com).
 A yau cikin wannan kasidar, zamu yi muku bayani dalla-dalla akan yanda zaku iya hada wannan Bank account naku da kuma PayPal account  ta hanyar amfani da Master card dinku. Domin hada asusun banki da kuma na PayPal, akwai wasu hanyoyi  biyu zuwa ukku da ake bukatar mutum ya bi. Ga wadannan hanyoyi kamar haka:


1. Shiga tare da yin Log in (ko kuma register idan ba’a bude ba) a PayPal account din.



2. Shiga inda aka sanya Wallet daga saman page din (idan a computer ne). In kuma da Waya ne aka shiga, to sai an fara shiga wajen menu sannan sai a shiga cikin Wallet din.




3. Shiga inda aka sanya Link a payment method sai a zabi select a credit or debit card. A Zabi irin card din da ake amfani da shi (Master card ko kuma Visa).



4. Bayan an zabi card idn sai a shigar da bayanan card din. Wadannan bayanai sun hada da lambar da ke a jikin card din, lokacin da zaya bar yin aiki (wato expiry date) da kuma wata lamba da ake cema security number wacce zaku iya samunta daga bayanka card din (zaku ganta guda ukku ce)

 



Idan kuma da waya ne kuke bukatar amfani, ta muna baku shawara da ku yi amfani da application na paypal na Android ko kuma na iPhone wanda zaku iya samu a Play Store (android) ko kuma Apple Store (iPhone). Wadannan apps din sun fi saukin amfani a waya fiye da shiga ta browser.
  
Ku kasance da mu a cikin kasidardarmu ta gaba ta Damammaki a Inernet inda zamu yi tsokaci akan ire-iren damammakin da zaku iya amfani da su wajen samun wani a abun amfani a saman Internet.

Comments