1 . Saukin fahimta
2 . Bayyana wasu
dokoki na programming ta yanda za’a iya gane su cikin sauki
3 . Wadatuwar abubuwan da ake bukata domin yin programming
din (kamar software da ake rona program din da ita)
Shafin #SADARWA na farin cikin sanar da kowa da kowa, musamman wadanda ke bukatar koyon harkar Programming da Web_Design, cewa mun fara rajistar sabbin dalibai a ajujuwansu na #Virtual_Class kamar haka:
Showing posts with label Programming. Show all posts
Wednesday, 10 January 2018
SANARWA!! SANARWA!!!
Shafin #SADARWA na farin cikin sanar da kowa da kowa, musamman wadanda ke bukatar koyon harkar Programming da Web_Design, cewa mun fara rajistar sabbin dalibai a ajujuwansu na #Virtual_Class kamar haka:
1. HTML (Intro to Web Design)
2. Java Programming 1 (Intro)
Kamar dai yanda kuka sani, wadannan classes namu muna gudanar da su a kan dandalin WhatsApp, a inda mukan bayar da handouts tare da kuma gabatar da lectures (Video tutorials) a kan ko wane handout da muka bayar.
Ga dukkan mai sha'awar shiga wannan aji namu, sai ya tuntubemu ta inbox
ko kuma ta hanyar wakilanmu a dandlin sada zumunta na WhatsApp ta 07061599050 domin karin bayani akan yanda za'a iya yin rajistar da kuma lokacin da wadannan darussa zasu soma.
Friday, 22 September 2017
YANDA SOFTWARE ZATA IYA SAUKAKA AYYUKA NA YAU DA KULLUM
A
cikin kasidarmu da ta gabata, mun yi sharhi na musamman a kan HAKIKANIN MA'ANARSOFTWARE, inda muka kawo cikakken bayani akan software, ma'narta, da kuma yanda
take aiki domin gudanar da wani abu da muke bukatar yi da computer.
A cikin wannan kasidar, kamar yanda muka
alkawarta, zamu yi sharhi ne akan yanda software zata iya taimaka mana wajen
saukake wasu ayyuka da muke yi na yau da kullum.
Zamu iya cewa kusan dukkan wani abu da mu ke
yi a rayuwarmu ta yau da kullum, babu inda computer ba zata iya shiga ba domin
saukaka yanda abubuwa ke gudana. Amma kuma har ya zuwa yanzu, ba kowa ne ya
fahimci hakan ba, ta yanda zaka ga mutum na kwashe awanni wajen yin wani aiki
(kamar tattara bayanai ko kuma gudanar da wani bincike ko lissafi), duk da cewa
kuma zasu iya amfani da computer ko kuma wayar hannu da zata iya rage lokacin
da za'a iya dauka domin yin wannan aiki. Za'a iya yin hakan ne kuma ta hanyar
hada ma mutum software da zata taimaka mishi wajen yin wannan aiki a cikin
computer ko kuma wayar hannu.
Shin ko kai dan kasuwa ne? Kuma kana shigar da
bayanan kasuwancinka a cikin littafi domin yin lissafi a ko wace rana ko kuma
bayan wani lokaci? Sanin kowa ne a duk lokacin da akan bukaci yin wannan
lissafi tare fitar da uwa ko kuma riba daga cikin wannan bayanai da aka sanya a
littafi, ana daukar lokaci sosai! Wani lokacin ma sai kaga anyi kuakure wajen
ragewa ko kuma wani abu. A maimakon kawai ka rika chatting computarka ko kuma
wayarka, don mi ba za' a yi maka sodtware ba wacce zata rika yi maka wannan
aiki ba tare daka wahala wajen yinshi ba? Wannan abu ne mai matukar sauki kuma
da dama daga cikin 'yan kasuwa da suka waye a harkar computer suna yin hakan ne
domin rage yawan kudi da kuma lokaci da sukan kashe wajen yin lissafi.
Shin ko kun san cewa computocinku da kuma wayoyinku
zasu iya taimaka muku akan kusan duk wani aiki da kuke yi? Ko wane irin abu ne
kuke yi kuma kuke ganin wannan na ci.muku lokaci, to zaku iya bukatar a yi muku
software ta computer ko kuma ta waya wacce zata ita yi muku wannan aikin ba tare
da kun bata lokutanku ba.
Akwai
da dama daga cikin mutane wadanda duk da cewa sun san amfanin software da kuma
aikin da zata iya, sukan yi tunanin cewa hadata ko kuma designing dinta na da
tsada sosai, shi ya sanya sun kwammace su rika yin abubuwansu da hannu (manual)
maimakon yin amfani da computer ko kuma wayar hannu. Muna tabbatar muku da cewa
wannan abu kwata-kwata ba haka yake ba. Domin a yanzu, farashin software ya
sauko sosai, inda a Nairarka 2000 zuwa sama za'a iya hada ma software wacce
zata yi maka duk wani abun da kake bukata a saukake.
Shin ko akwai wani aiki da kake yi wanda kake
mamakin yanda zaka iya amfani da software wajen saukake wannan aiki? Ka yi
comment a nan kasa, ko kuma ka turo mamu tambayarka a sakon email ko shafinmu
na Facebook ko kuma ta whatsapp ta hanyar wannan lambar +2347061599050 ( 07061599050).
Tuesday, 19 September 2017
HAKIKANIN MA'ANAR SOFTWARE
Za ku yi mamakin cewa, har
yanzu a wannan lokacin da muke ciki,
akwai mutanen da basu san ma mi ake cema Software ko kuma application ba. Wasu
mutanen kuma duk da cewa sun san mi ake nufi da software ko kuma application,
to amma dai sun yi abun gurguwar fahimta, ta yanda wannan fahimtar ta hanasu ma
su san hakikanin amfani da kuma ayyukan da software ko kuma application zaya
iya yi musu a cikin rayuwarsu ta yau da kullum.
A cikin wannan kasida ta musamman, zamu yi tsokaci akan Software da kuma
irin tasirin da take da shi a duniyar computer.
Ba
komai ne ake kira da Software ko kuma Application ba, sai wasu rubutattun
dokoki ko kuma jerin ka’idoji wadanda computer zata iya bi domin aiwatar da
wani abu ko kuma wani aiki da muke so ta yi mamu. Kamar yanda wata kila zaku
iya sani, computer ba zata taba iya yin wani aiki ba da Karin kanta, har dai sai in an sanya ta tayi, to ana sanya
computer ta yi wani aiki ne ta hanyar amfani da software, wanda kuma a cikin
wannan software ne ake rubuta ka’idoji ko kuma matakai daya bayan daya da
computer zata iya bi domin aiwatar da wannan aiki.
Ba
lallai ne kowa ya fahimci jawabin da muka yi a sama ba, amma bari mu yi amfani
da wani misali domin fayyace ko kuma bayyana yanda software take da kuma yanda
take aiki. Misali, kaddara cewa akwai wani sabon girki da ake bukatar mutum
yayi, wannan girki kuma ba lallai ba ne ace mutum ya san yanda ake yinsa. To
amma akwai wata takarda da ke dauke da matakai ko kuma ka’idoji da mutum zaya
bi tun daga dora tukunya a saman wuta, har ya zuwa kammala girkin. Abu mafi
sauki shine mutum ya dauki wannan takardar tare da bin wannan matakan girki da
aka zayyana a cikinta daya bayan daya, domin cimma gurinsa na kammala wannan
girki kamar yanda aka bukace shi. Mutum zaya rika karanto layi daya na rubutu a
ko wane lokaci tare da aiwatar da abin da aka umarce shi da yayi a cikin wannan
layin, kafin ya iya matsawa zuwa layi na gaba. Haka za yai ta bin wadannan
dokokin daya bayan daya kuma yana aiwatar da su har sai ya je karshensu. Wannan
shine zaya kai shi ga karshen wannan girki da ya soma yi.
To kamar yanda muka bayyana a cikin
wannan misalin na sama, ita software ita ce kamar waccan takardar mai dauke da
dokokin da za’a iya bi domin aiwatar da girkin, a yayin da kuma ita computer
ita ce kamar mutumin da zaya rika karanta wadannan dokokin tare da aiwatar da
su daya bayan daya har sai an kai karshensu. Idan mun fahimta sosai da wannan
misali da aka bayar, zamu gane cewa ba komai bane software ko kuma application
fa ce wani file mai dauke da wasu dokoki ko kuma jerin ka’idoji wadanda
computer zata iya karantawa, ta fahimce su, tare da kuma aiwatar da su daya
bayan daya har sai ta cimma karshen su. Zuwa karshen wadannan jerin dokoki ko
kuma ka’idoji da ke a cikin software, shine ke nuna cewa computer ta zo karshe
ko kuma ta kammala abin da ake bukatarta da ta aiwatar.
Kaddara muna so mu rubuta wani
application ko kuma software wacce zata rika yin kiran sallah duk idan lokacin
sallah yayi, zamu iya rubuta dokokin ko kuma ka’idojin a cikin wannan software
kamar haka:
1 .
Duba lokaci
2 . Idan lokacin sallah ne, to yi kiran sallah
3 . Idan kuma ba lokacin sallah bane, to sake
jaraba duba lokacin bayan wasu mintuna
Kamar yanda muka rubuta wadannan
dokoki a sama, haka computer zata yi ta karantawa tare mai-maita wadannan
dokokin har sai lokacin da muka bukaci tsayar da ita wannan software (ko kuma
idan mun cireta daga cikin wayar ko computar). Wadannan jerin dokoki su ne ake
kira da Algorithm a fannin ilimin
computer, wato wasu jerin dokoki ko kuma ka’idoji da za’a iya bi domin aiwatar
da wani abu. Shi kuma wannna Algorithm
bayan mun tsara shi, sai mu yi amfani da wani yaren computer (wato programming language) domin sake rubuta
shi ta yanda computer ko kuma waya (mobile phone) zasu iya fahimtar abin da muke
nufi akan ko wane layin doka da muka rubuta.
Wannan
shine sharhi na musamman akan Software ko kuma application, in Allah ya so , a
cikin kasidarmu ta gaba, zamu kawo cikakken bayani akan yanda zaku iya amfani
da software ta waya ko kuma ta computer wajen magance wasu matsaloli naku na
ayyukan yau da kullum ko kuma saukake hanyar da zaku iya bi wajen aiwatar da
wasu abubuwan.
Wednesday, 28 June 2017
DA WANE PROGRAMMING LANGUAGE MAI KOYO YA KAMATA YA FARA?
A cikin kasidarmu da ta gabata a kan programming, mun yi Magana
ne akan Yanda ake koyon programming da kuma irin matakan da ya kamata mai koyon
programming ya bi domin samun sauki a wajen koyon. A cikin wannna kasida, zamu
yi Magana ne akan irin programming language din da mutum ya kamata ya fara da
shi, a yayin da yake son fara koyon programming.
Kamar yanda muka fada a kasidarmu da ta gabata, duk da cewa
programming language ba shine ake koyo ba kai tsaye (ana koyon yanda ake yin
programming din ne kawai), dole ne idan zaka koyi programming sai kayi amfani
da wani yaren (programming language) domin auna fahimtarka akan abin da ka koya
(practice). Akwai wasu programming da akan baiwa masu koyo shawarar da su fara
amafani da su wajen koyon yanda ake programming. Wadannan Programming languages
akwai dalilai da dama da suka sanya ake bada shawarar a fara da su. Kadan daga cikin wadannan dalilai sun
hada da:
1 . Saukin fahimta
2 . Bayyana wasu
dokoki na programming ta yanda za’a iya gane su cikin sauki
3 . Wadatuwar abubuwan da ake bukata domin yin programming
din (kamar software da ake rona program din da ita)
4 . Yawan mutane da ke amfani da programming language din
(ta yanda zaka iya samun wadanda zasu taimaka maka idan ka samu wata ‘yar
matsala da ka kasa ciyo kanta)
Wadannan da ma wasu dalilan sune ke sanyawa ana bada shawara
akan programming language da mutum ya kamata ya fara amfani da shi a yayin da
yake koyon programming.
Kadan daga cikin wadannan programming language din sun hada
da:
1 . Java
2 . HTML
3 . C++
4 . Visual Basic
Amma dai mu wadanda muka fi bada shawara a kansu sune Java da kuma HTML.
Kawo yanzu, a cikin jerin kasidunmu na programming, mun kawo
bayanai akan Manya-manyan kura-kurai ukku da masu koyon programming kan tafka,
Yanda ake koyon programming da kuma programming language din ya kamata a fara
amfani da shi wajen koyon programming, a cikin kasidarmu ta gaba a kan
programming, zamu yi Magana akan software ko kuma applications da ake amfani da
su wajen rubuta Java program.



Comments
Post a Comment