Ba
komai ne ake kira da Software ko kuma Application ba, sai wasu rubutattun
dokoki ko kuma jerin ka’idoji wadanda computer zata iya bi domin aiwatar da
wani abu ko kuma wani aiki da muke so ta yi mamu. Kamar yanda wata kila zaku
iya sani, computer ba zata taba iya yin wani aiki ba da Karin kanta, har dai sai in an sanya ta tayi, to ana sanya
computer ta yi wani aiki ne ta hanyar amfani da software, wanda kuma a cikin
wannan software ne ake rubuta ka’idoji ko kuma matakai daya bayan daya da
computer zata iya bi domin aiwatar da wannan aiki. Ba
lallai ne kowa ya fahimci jawabin da muka yi a sama ba, amma bari mu yi amfani
da wani misali domin fayyace ko kuma bayyana yanda software take da kuma yanda
take aiki. Misali, kaddara cewa akwai wani sabon girki da ake bukatar mutum
yayi, wannan girki kuma ba lallai ba ne ace mutum ya san yanda ake yinsa. To
amma akwai wata takarda da ke dauke da matakai ko kuma ka’idoji da mutum zaya
bi tun daga dora tukunya a saman wuta, har ya zuwa kammala girkin. Abu mafi
sauki shine mutum ya dauki wannan takardar tare da bin wannan matakan girki da
aka zayyana a cikinta daya bayan daya, domin cimma gurinsa na kammala wannan
girki kamar yanda aka bukace shi. Mutum zaya rika karanto layi daya na rubutu a
ko wane lokaci tare da aiwatar da abin da aka umarce shi da yayi a cikin wannan
layin, kafin ya iya matsawa zuwa layi na gaba. Haka za yai ta bin wadannan
dokokin daya bayan daya kuma yana aiwatar da su har sai ya je karshensu. Wannan
shine zaya kai shi ga karshen wannan girki da ya soma yi.
To kamar yanda muka bayyana a cikin
wannan misalin na sama, ita software ita ce kamar waccan takardar mai dauke da
dokokin da za’a iya bi domin aiwatar da girkin, a yayin da kuma ita computer
ita ce kamar mutumin da zaya rika karanta wadannan dokokin tare da aiwatar da
su daya bayan daya har sai an kai karshensu. Idan mun fahimta sosai da wannan
misali da aka bayar, zamu gane cewa ba komai bane software ko kuma application
fa ce wani file mai dauke da wasu dokoki ko kuma jerin ka’idoji wadanda
computer zata iya karantawa, ta fahimce su, tare da kuma aiwatar da su daya
bayan daya har sai ta cimma karshen su. Zuwa karshen wadannan jerin dokoki ko
kuma ka’idoji da ke a cikin software, shine ke nuna cewa computer ta zo karshe
ko kuma ta kammala abin da ake bukatarta da ta aiwatar.
Kaddara muna so mu rubuta wani
application ko kuma software wacce zata rika yin kiran sallah duk idan lokacin
sallah yayi, zamu iya rubuta dokokin ko kuma ka’idojin a cikin wannan software
kamar haka:
1 .
Duba lokaci
2 . Idan lokacin sallah ne, to yi kiran sallah
3 . Idan kuma ba lokacin sallah bane, to sake
jaraba duba lokacin bayan wasu mintuna
Kamar yanda muka rubuta wadannan
dokoki a sama, haka computer zata yi ta karantawa tare mai-maita wadannan
dokokin har sai lokacin da muka bukaci tsayar da ita wannan software (ko kuma
idan mun cireta daga cikin wayar ko computar). Wadannan jerin dokoki su ne ake
kira da Algorithm a fannin ilimin
computer, wato wasu jerin dokoki ko kuma ka’idoji da za’a iya bi domin aiwatar
da wani abu. Shi kuma wannna Algorithm
bayan mun tsara shi, sai mu yi amfani da wani yaren computer (wato programming language) domin sake rubuta
shi ta yanda computer ko kuma waya (mobile phone) zasu iya fahimtar abin da muke
nufi akan ko wane layin doka da muka rubuta
Comments
Post a Comment