Ku shiga YouTube din tare da nemo Video din da
kuke bukatar saukowa
Showing posts with label YouTube. Show all posts
Monday, 2 April 2018
Hanya Mafi Sauki Da Zaku iya Download Na YouTube Video
Ya zuwa yanzu akwai hanyoyi
da dama da ake amfani da su domin sauko da video kai tsaye daga YouTube
zuwa wayoyin ko kuma computocin mutane. Sai dai kuma mafi yawa daga cikin
wadannan hanyoyi suna bukatar ko dai mutum yayi amfani da computer wajen sauko
da videon ko kuma yayi amfani da babbar waya. A cikin wannan kasidar ta mu ta
wannan lokaci, zamu nuna muku yanda zaku iya sauko da video kai tsaye daga
YouTube zuwa wayoyinku ko wadanne iri ne.
Akwai wani sabon shafi da aka fito da shi wanda ke baiwa mutane
damar sauko da video kai tsaye daga shafin YouTube zuwa cikin wayoyinsu ba tare
da sun bar shafin YouTube din kai tsaye ba. Sabanin wasu shafukan da aka sani a
baya wadanda sukan bukaci mutum da ya kwafi address na videon da yake bukata
tare da sanya wannan address din a cikin website din nasu, shi wannan website
yana baku dama kai tsaye ba tare da kun kwafi ko wane address ba.
Domin sauko da video ko ma wace iri ce daga YouTube, sai ku
bi wadannan matakan kamar haka:
1.
Ku shiga YouTube din tare da nemo Video din da
kuke bukatar saukowa
2.
Bayan kun nemo viden sai ku je wajen da ake
sanya address zaka ku ga an rubuta kamar haka:
https://m.youtube.com/.....
Sai ku canja m. din zuwa www.vd Wato address din zaya canja daga
https://m.youtube.com/.... Zuwa
https://www.vdyoutube.com/....
3.
Kai tsaye wannan zaya nuna muku inda zaku taba
domin yin download na wannan video din. Sai ku zabi format din da kuku bukata
domin yin download (ko mp4, ko kuma 3gp).
Wadannan sune matakan da zaku iya bi kai tsaye domin sauko
video daga shafin YouTube ya zuwa wayoyinku na salula.

Comments
Post a Comment