1 . Hasashen Password: Kamar yanda
muka bayyana a cikin waccan kasidar, mutane musamman hackers sun gano cewa
akwai da yawa daga cikin mutane da ke yin amfani da lambobin wayoyinsu,
sunayensu, ranakun haihuwarsu, lambar rajistar ta makaranta (school
registration number), da dai sauransu, a matsayin password dinsu. Wannan ne ya
sanya hackers ke amfani da wannan babbar dama inda kai tsaye idan suna bukatar
hacking na account din mutum zasu fara da wannan hanyar ta Hasashen password
din na mutum ta hanyar amfani da sunansa, lambar wayarsa da dai sauransu. Domin
kauce ma wannan hanyar, sai mutum ya tabbatar da cewa bai yi amfani da wani
bayani na shi a matsayin password dinsa ba.
2 . Zamba cikin aminci (Social Engineering):
Zamba cikin aminci ko kuma social engineering a turance, wata hanya ce mai
zaman kanta wacce hackers ke amfani da ita domin yin hacking computer ko kuma
account na mutum. Wannan hanya dai tana daya daga cikin hanyoyi mafi sauki
wajen yin hacking, a inda hacker ke amfani da kusancinsa da wanda yake son yi
ma hacking din wajen satar wasu bayanai da zaya iya amfani da su wajen gudanar
da wannan ta’asar ta sa. Akwai hanyoyi da dama da ake bi wajen satar password a
wannan salon hacking na zamba cikin aminci. Wadannan hanyoyi sun hada da kallon
mutum a yayin da yake sanya password (eaves dropping a turance), amsar wayar
mutum a canja mishi password (ta hanyar amfani da password recovery) ko kuma ta
hanyar yin installing din wani application a cikin wayar ko kuma computar mutum,
wannan application zaya rika yin liken asiri ne tare da tura wasu bayanai zuwa ga
hacker din.
3 . Yaudara: Wannan kuma wata sabuwar hanya
ce da ake iya yin hacking din account na mutum ta hanyar bukatarshi da ya bayar
da wasu bayanai na sa. Salon da aka fi amfani da shi a wannan lokacin shine,
mutum zaya je a account naka ya sanya username naka, sannan sai ya bukaci yin
password recovery inda za’a tura wani code zuwa wayar mai wannan account din
domin ayi amfani da shi wajen sauya wani password din. Da zaran shi wannan
hacker ya tabbatar da cewa an tura wannan code zuwa ga shi mai wannan account,
sai ya kira shi a waya tare da nuna mashi cewa wai wani registration ne yake yi
to sai aka samu matsala yayi kuskuren lamba wajen sanya lambar wayarsa sai ta
fado shi mai account din, inda zaya bukace shi da ya taimaka ya bashi wannan
code da aka turo masa domin ya ci gaba da yin rajistar. Da zarar shi wannan mai
account ya kuskura ya bashi wannan code din, to shi ke nan shi kuma bukatarsa
ta biya, kai tsaye kawai zaya tafi ya canja mashi password tare da mallakar
wannan account din na mutum ko kuma yayi duk wani abin da yake bukata da shi.
Da fatan zaku yi amfani da wannan ilimin wajen kare kanku ba
wajen cutar da wasu ba. Domin a dokar Nigeria, duk wanda yayi hacking din computer ko kuma
account din wani to hukuncinsa shine daurin shekara 5 ko kuma tara ta Naira
milyan 7. Da fatan za’a kiyaye!
Comments
Post a Comment