HOSTING da kuma DOMAIN a Harka Web Design

Kalmomi biyu da a wasu lokuta suke yin wuyar fahimta ga masu koyon harka Web Design (ko kuma Web Development) sune HOSTING da kuma DOMAIN. Shin minene ma’anar HOSTING da kuma DOMAIN? Mi ya bambanta su? Kuma mi ke amfanin ko wanensu a harkar Web Design?
A kasidarmu ta wannan lokaci, zamu war-ware muku zare da abawa dangane da wadannan kalmomi guda biyu.
A cikin wasu kasidojinmu da muka kawo muku a baya, mun yi jawabi akan cikakkiyar ma’anar website da kuma abubuwan da suka hadu domin bada website din baki dayansa (Taba nan domin karanta wannan kasida). Kamar yanda muka fada a cikin waccan kasidar, akwai abubuwa da dama da suka hadu suka bada website. Wadannan abubuwa kuwa sun hada html files din da aka yi amfani wajen tsara shafukan site din, hotuna ko kuma pictures da aka yi amfani da su, videos da aka sanya da dai sauran abubuwan da za’a iya samu a cikin website.
Shin dukkanin wadannan abubuwan da muka zayyana a ina ne mutum ke ajiye su? Kuma ta yaya 
 sauran mutane ke iya ganinsu bayan ka sanya su a cikin website din?
 Hanyar da ake bi wajen dorawa ko kuma yin uploading din duk wasu abubuwa da website ke bukata ko kuma abubuwa da suka hadu suka bada website (kamar html, css, pictures, videos, rubutu da dai sauransu) ita ce ake kira da HOSTING.  Ma’ana hosting na nufin dora website da kuma kayayyakinsa a saman internet.
Kamar yanda mafi yawancin mutane ke yi, idan suna bukatar hada website sukan fara designing din sa ne a cikin computer dinsu (wato offline ke nan). Bayan sun kammala designing ko kuma hada shi wannan website din (wato sun kammala designing na website din tare da sanya duk wasu abubuwansa a ciki), to mataki na gaba shine su dora website din a saman internet (wato online  ke nan). Ita wannan hanya da ake bi wajen dora website a saman internet shi ake kira da HOSTING
To bayan kuma ka dora website a saman internet ta yaya za’a yi mutune su iya ganin wannan website din naka?
Hanyar da mutum zaya bi domin tabbatar da cewa za’a iya gani ko kuma ziyartar website dinsa shine ta hanyar samawa  website dinsa  abin da ake kira da DOMAIN name. Shi Domain Name shine ke matsayin address din da za’a iya bi domin gano inda website din yake a saman internet. Zamu iya alakanta HOSTING da wayar hannu (ko kuma mobile phone), DOMAIN name kuma zamu iya alakanta shi da lambar waya ( ko kuma SIM card). Idan ka sayi wayar hannu (ko kuma idan kayi hosting) to dole ne ka sayi layi domin mutane su yi amfani da wannan lambar layin domin samunka (wato a nan ma dole ka yi amfani da Domain name domin bayyana  address din da za’a bi domin ziyartar shafinka na  internet).
Domain name da kuma Hosting akwai na kudi akwai na kyauta. Mafi yawancin kamfanonin da ke bayar da free Domain suna bayar da free Hosting.
 Misali Blogger yanda bayarda da free Hosting (inda mutum zaya iya dora files da sauran abubuwa a cikin website), suna kuma bayar da free Domain (wato address din website din, wanda ke karewa da .blogspot.com ).  Akwai kuma Wapka wanda shima yana bada free Domain ( .wapka.com) da kuma free hosting inda mutum zaya iya dora files dinsa.
Akwai kuma website da suka kware wajen harkar siyar da Hosting da kuma Domain name (misali Bluehost, Web4Africa da dai sauransu), inda mutum zaya siya akan wasu kudi, su kuma sais u bashi wannan domain da kuma hosting din na dan wani lokaci (misali shekara guda).
Bambancin free da kuma na siya a nan shine, na free ba zaya baka dam aka yi duk wani abun da ka bukata ba, a yayin da kuma na siya zaya baka dama ka yi design tare da tsara website dinka yanda ka bukata.

Comments