A yau kasidarmu ta programming ta
zata yi Magana ne akan wasu manyan kura-kurai da masu koyon programming kan yi
a yayin da suke koyon programming din. Wadannan kura-kurai sukan sanya mutum ya
kasa sanin inda matsalarsa take wajen koyon programming din, wanda a karshe
hakan kan sanya mutum ya yada kwallon mangwaro domin ya huta da kuda -wato mutum ya tattara koyon gaba daya ajiye
a waje guda domin yana ganin wannan abu wahalarsa tayi yawa don haka ba zai iya
koyo ba.
Wadannan manyan kura-kurai sune
kamar haka:
1.
Koyon Programming Language a maimakon koyon
yadda ake programming
2.
Dole ne mutum yasan komai a programming kafin ya
fara yin wani abu
3.
Rashin yin bincike da kuma tuntubar masana.
A cikin wannan kasida, zamu dauki
wadannan kura-kurai daya bayan daya domin yin cikakken bayanai akansu da kuma
bada shawarwari akan yanda mutum zai yi domin kauce ma wadannan matsaloli.
1.
Koyon
Programming Language a maimakon koyon yanda ake Programming
Programming Language shine yaren da ake amfani da shi wajen baiwa
computer umarni domin tayi wani aiki da ake bukatar tayi kamar tura sakon
message, connecting da network, lissafi ko kuma calculations da dai sauran
aiyukan da computer/waya zasu iya yi. Programming languages suna da matukar yawa,
kadan daga cikinsu sun hada da Java,
C, C++, Ruby, Pythons, Visual Basic da dai sauransu. Shi kuma Programming shine ainahin
ilimi ko kuma hanyar da ake bi domin rubuta program ko kuma code (wato yanda
ake yin coding).
A maimakon kaji mai koyon
programming yana tambayar “ta yaya zan
yi amfani da Programming Language wajen sanya computer ta yi mani abin da nike
so?” a mafi yawancin lokaci, zaka ji mai son koyon programming yana
tambayar “da wane programming language
ya kamata ya fara?” ko kuma “Programming
language nawa ka iya?” Duk da cewa ba wani matsala bane mutum ya tambayi ko
da wane programming language zaya fara da shi a matsayinsa na wanda zaya fara
koyo, babbar matsalar itace, ka dauka cewa wannan Programming Language shine
kake koyo ba yanda aka coding ba. Abin da ya kamata ka baiwa karfi shine yanda
ake programming ko kuma yanda ake rubuta code (coding). Shi Programming (ko
kuma coding) ya kunshi sanin ka’idoji da kuma dokoki da ake amfani wajen rubuta
program (code) ko ma a wane yare ne. Idan ku ka yi duba sosai zaku ga cewa,
kusan dukkanin programming languages suna kamanceceniya da juna, wato a ko da
yaushe zaka ga kamar duk iri daya ne, sai dai dan bam-banci kadan da ba’a rasa
ba. Wannan ne ya sanya idan ka san yanda ake rubuta programming to koyon
programming language ko ma wane iri ne ba zai yi maka wahala ba.
2. Dole ne mutum yasan komai a
programming kafin ya fara yin wani abu
Wani babban kuskure kuma da masu
koyon programming suke yi shine, tunanin cewa wai ba zasu iya komai ba har sai
sun san komai a wannan Programming language din. Wannan ko kadan ba haka abin
yake ba, domin babu wani programmer da zaya ce wai shi yasan komai a cikin
programming. Asali ma dai, mafi yawancin programmers suna fara koyon yanda zasu
yi wani abin ne idan bukatar hakan ta taso, wato suna koyon sabon abu ne a ko
wane irin language a lokacin da suke bukatar amfani da wannan abun. Misali,
mafi yawan lokaci, sai idan programmer ya bukaci yi ko kuma an bashi kwangilar
yin application, misali kuma ace application din zaya yi amfani da network, to
a wannan lokacin ne zaya fara koyon yanda ake sanya function na network cikin
application ko software a wannan language din. Ko kadan ba za ka ji programmer
yace maka ba zai iya yin aiki ba saboda bai san yanda ake yi ba, a’a zaya karba
ne sannan ya dukufa koyon yanda zaya yi hakan tun da dama ya san dokoki ko kuma
ka’idoji da ake bi wajen yin programming. Shi ma mai koyon programming abin da
ya kamata ya rika yi shine, a duk lokaci ya baiwa kanshi wani aiki ko kuma
exercise akan yanda zaya iya hada application ko kuma software da zata yi wani
abun. Wannan itace hanya mafi sauki kuma mafi sauri da ake koyon programming.
3.
Rashin yin
bincike da kuma tuntubar masana
Wani kuskuren kuma da masu koyon
programming kan tafka shine, rashin yin
bincike Karin ilimi akan programming da kuma cudanya ko kuma gogaiya
da wadanda suka san programming din. Hanya mafi sauki da zaka iya war-ware wata
matsalarka dangane da programming itace ta hanyar tuntubar masana, domin sune
zasu iya ganowa tare da fadamaka matsalarka cikin kankanen lokaci. Dole ne kuma
mai koyon programming ya kasace mai son sanin sabbin abubuwa, domin ta haka ne
zaka iya samun kwarin guiwar koyon shi programming din. Hanya mafi sauki da
zaka iya yin bincike tare da neman taimako daga masana, ita ce Internet. Domin
yin bincike, Google shine hanya mafi sauki a gare ka. Domin cudanya da wadanda
suka san programming sai ka binciki websites da ke zama a matsayin dandali na
programmers kamar stockoverflow.com, a inda zaka iya yin tambayarka ko wace iri
ce, take wani ya amsa maka a cikin kankanen lokaci. Muma a shafin sadarwa a
shirye muke a ko da yaushe domin taimakawa duk wani mai neman taimako a wannan
fanni da ma sauran fannuka.
Wadannan Kura-kurai guda ukku da
muka kawo tare da shawarwari akan yadda zaku kauce masu, zasu taimake ku sosai
wajen koyon programming da kuma programming language ko ma wane iri ne.
Comments
Post a Comment