Matsalar Downloading daga Play Store

A cikin 'yan lokutan nan, akwai da yawa daga cikin mabiyan wannan shafi mai albarka da ke kokawa sosai akan yanda matsalar da manhajar nan da ake downloading android app da ita (wato Play Store) ta ke basu matsala a yayin da suke son yin downloading din application na Android. Mun yi nazari kuma mun fahimci dalilin wannan matsalar, ga kuma hanyar da zaku bi wajen war-ware ta mun kawo muku a cikin wannan kasidar ta mu.
Ita dai wannan matsalar tana sanyawa idan mutum ya shiga cikin Play Store din domin yin download na wani, to ko da ya zabi wannan app da zaya yi downloading, to a maimakon  ya fara downloading din, sai kawai ya tsaya yana ta loading, daga nan kuma baya wucewa sai dai mutum ya gaji da jira ya rufe application din.
Domin war-ware wannan matsalar, sai a bi wadannan saukakan matakan kamar haka:
1. Ka shiga a cikin Settings na wayarka.
2. Ka duba inda aka sanya Apps ko kuma Applications sai ka shiga wajen
3. Ka duba daga kasa domin gano inda app din Play Store yake, sai ka taba shi
4. Wani wajen zaya bude kamar na cikin hoton nan
4. Sai ka taba inda aka sanya Force Stop, zaya tambaye ka sai ka sanya Yes
5. Daga nan kuma sai ka taba inda aka sanya Clear cache ko kuma Clear data domin goge abubuwan da suke cikin shi wadanda suka sanya matsalar, shi ma zaya tambayeka, sai ka sanya Yes.
6. Sai ka sake dubawa daga sama akwai inda aka sanya Enable, sai ka taba wajen
7. Sai ka duba ka gani idan ya gyaru, idan kuma bai bari ba, to sai ka sake duba wani app din da ake kira Google Play Service, shima sai ka yi mashi kamar yanda ka yi ma wannan din.

Comments