TA YAYA INTERNET YAKE AIKI

Shi Internet ta wurin aikawa da sakonni yana amfani da wani abu wanda ake kira Internet Protocol shi Internet protocol shine yake nuna DATA (information) dinka zasu ko daga ina suke misali:- karubuta wasika a computa ta 192.168.45.2 zaka aika 192.168.87.45, ko idan zaka aika da wasika irin ta gargajiya bawai zakaje ka ajje wasikar a post office bane, a’a yana bukatar karubuta adireshin da wasikar zataje, to shima haka internet protocol yake a internet, yana da nambobi guda hudu, kumka kowace namba tana kasa da 256, nambobin suna nan kamar haka:- 192.112.36.5  ko  128.174.5.6     kaga nambobin farko suna nuna daga wane irin network sako yake, na dama daga karshe shike nuna daga wacce computa bayanin yafito,  misali:- kana kana cyber cafĂ© a computer ta 12 sannan network din su shine 128 kaga IP naka zai zama 128.XXX.XXX.12.
Idan baka gane misalign farko bag a dan gajeren misali ko zaka gane:- misali kana da handset, da namba, sai ka rubuta sako ka aika wa wani, shi wanda ka aikawan, ya cire layinsa daga cikin handset dinsa, to lokacin da ka aika da wannan sakon, sakon zai ta fi network (misali MTN), idan yaje can, sai su ajje wannan sakon har lokacin da wanda ka aikawa sakon yasa layinsa, yana sa layin sa, zai ga sakon da ka aiko mai, ya karanta. To shima Email haka yake, idan ka budo email dinka ka, ka rubuta wasika zuwa ga wani, wanda ka aikawa idan baya kan computer, to wannan wasikar zata ta fi wurin webserver (misali YAHOO), sun e zasu ajje wannan sakon, har duk lokacin da wanda ka aikawa sakon yaje yabudo email dinsa, sai sutoro maid a wasikunsa ga b daya , ya karantasu, zasu turo masa net a hanyar WEB BROWSER (wanda zanyi Magana anan gaba), bayan sun turo masa shi kuma sai yakaranta ta anan, web browser din.

Comments