Gaba daya website ko kuma shafin internet za'a iya raba shi gida biyu ta
la'akari da yanda ake hada shi (wato web
design) da kuma abubuwan da ake amfani da su wajen hada shi. Hada website
ko kuma web design ya kasu zuwa gida biyu kamar haka:
1. Sashen da ake iya gani idan an ziyarci website din (wato Front-end)
2. Sashen da mutum wanda ya ziyarci website din baya iya gani (wato Back-end)
1. SASHEN DA AKE GANI IDAN AN ZIYARCI WEBSITE(FRONT-END)
Shi front-end, ko kuma sashen da ake gani idan an ziyarci website, ya kunshi
duk wani dubaru da ake iya amfani da su wajen yin designing ko kuma tsara duk
wani abu da ke a cikin website wanda idan mutum ya shiga website din zaya iya
gani. Abubuwan da za'a iya gani a cikin website sun hada da hotuna, videos,
rubutu, audio da dai sauransu. Ana amfani da abubuwa biyu zuwa uku ne wajen
designing din front-end na website.
Na daya, kuma jagora daga cikin wadannan abubwa da ake hada website da su,
shine HTML (Hypertext Markup Language). Shi HTML yare ne na computer (ko kuma
programming language) wanda kuma shine ginshiki na ko wane irin website da ka
sani, domin da shi ne ake designing din taswira, tsari ko kuma skeletal na
website. Da HTML ake amfani wajen sanya rubutu, hoto, video, malatsai (buttons),
wajen da mutum zaya iya sanya rubutu (wato textbox) da dai sauransu. Duk wani
abu da ka sani zaka iya tabawa ko kuma aiwatar da wani abu a cikin website ta
hanyar shi wannan abun, to ana amfani da HTML ne wajen sanya shi.
Baya ga HTML, abu na biyu da ake amfani da shi wajen yin design din
front-end (wato sashen da mutum ke iya gani) na website shine CSS (Cascading
Style Sheet). Shi CSS ana amfani da shi ne a website domin kayata website din ta
hanyar sanya wasu abubuwa kamar su kaloli (colors), zane da kuma positioning
(wato kuma tabbatar da cewa duk wani abu da aka sanya ta hanyar HTML to an dora
shi a inda ya kamata). Ba don CSS ba, to da website bai yi kyawon da muke ganin
shi da shi ba a yau, domin idan ba'a yi amfani da CSS ba wajen designing din
website, to kusan komi da ke cikin wannan website zaya fito ne cikin layi guda
ko kuma duk su hade a waje guda ta yanda ba zaka iya rarrabewa a tsakaninsu ba.
Daga CSS kuma, abu na uku da ake amfani da shi wajen yin designing na
front-end (wato sashen website wanda mutane kan iya gani) shine JavaScript. JavaScript shima yaren
computer ne (programming language) da ake amfani da shi wajen sanya website ya
zama dynamic, wato website mai sauya kamannu kuma wanda ke iya amsa bukatar
mutum (misali wajen yi rajista ko kuma Log in). Dynamic website shine website
wanda mutum zaya iya neman wani bayani (ko kuma searching din wani bayani) kai
tsaye a cikinshi kuma ya maido ma mutum da amsar wannnan bayani da ya nema. A
lokaci guda kuma ta yanyar javascript, za'a iya sanya website din ya nemi ko
kuma ya tambayi mutum wani bayani wanda za'a iya amfani da shi wannan bayani a
cikin website din ko kuma wani abin daban. In aka so, Za'a iya design na
website ba tare da javascript ba amma kuma yana da matukar amfani musamman ma
idan mutum yana bukatar wannan website ya zama dynamic.
Wadannan abubuwa guda uku, wato HTML, CSS da kuma Javascript, sune ake
amfani da su wajen designing ko kuma hada sashen website wanda mutane ke gani
idan sun ziyarci website din (wato front-end). Mutum wanda ya san wadannan
abubuwa guda ukku (HTML, CSS da Javascript) kuma yake hada website ta hanyar
amfani da su, shi ake kira da FRONT-END
DEVELPER wato wanda ke designing na sashen website wanda mutane ke iya gani
idan suka ziyarci wannan website din.
Mafi yawancin mutane kan shiga shafukan internet (wato web pages) a ko wane
lokaci, amma ko sau daya basu taba damuwa da cewa shin wai duk wadannan
abubuwan da suke gani a cikin wadannan shafukan ta yaya ake hada su ne? kuma ta
yaya wasu ke iya ziyara tare da ganin abin da ke website din? Shin wai bayanan
da a ko da yaushe muke sanyawa kamar hotuna, videos da kuma rubutu a ina suke
tafiya ne? Duk da cewa wasu mutanen sukan yi irin wadannan tambayoyi, kuma suna
son su san hakan, wata kila rashin wanda zaya war-ware masu zare da abawa shine
ya hana su samun wannan ilimin. Cikin wannan kasida ta 1 daga cikin jerin
kasidojin da zamu rika kawo muku akna website da kuma web design, zamu tattauna
ne akan shafin Internet (wato website) da kuma abubuwan da ya kunsa.
Kamar yanda mafi yawanci daga cikin masu karanta wannan kasidar suka sani
cewa, Website dai wani abu ne da ke kunshe da shafuka kala-kala wadanda kuma ko
wane daga cikin su yana dauke ne da wani bayani na musamman wanda dukkan wanda
ya ziyarce shi zaya iya gani. Website za'a iya cewa kamar wani akwati ne ko
kuma folder da ke dauke da shafuka daban-daban da aka ajiye a saman kafar
SADARWA ta internet, inda mutum kan iya connecting ga wannan folder din tare da
duba duk wani abu da ke a cikinta ( wato shafuka) ta hanyar ziyartar adireshin
da aka baiwa ita wannan folder din (website address).
Comments
Post a Comment