WEBSITE DESIGNER

MUN DADE MUNA SHIGA WEBSITES, TARE DA YIN WASU ABUBUWA KAMAR REGISTRATION, LOGIN, CHATTING, KALLON VIDEO, DA DAI SAURANSU, SHIN WAI DUK WADANNAN BAYANAN DA MUKE SANYAWA A CIKIN WEBSITES MI KE FARUWA NE A GARE SU BAYAN MUN SANYA SU? SHIN VIDEOS DIN DA MUKE KALLO DA KUMA SAURAN ABUBUWAN DA MUKE DOWNLOADING DAGA WEBSITE, A INA SUKE A AJIYE NE? 
Amsar wannan tambaya ita ce zata bamu cikakken bayanai da muke bukata domin fahimtar BACK-END. A cikin website akwai wani abu da ake kira da DATABASE wanda yake zama kamar wani rumbu ne na adana bayanai a saman website din. Duk wani abu da ka gani a cikin website, da ma abin da baka gani ba amma dai kuma yana cikin website din, to ana sanya shi ne tare da ajiye shi a cikin wannan rumbun bayanai na DATABASE. Misali, duk wani abu da ke cikin Facebook kamar hotuna, rubuce-rubuce, videos da dai sauran duka suna ajiye ne a cikin wannan rumbu na DATABASE. Shi kuma wannan rumbu ana sanya shi ne a cikin wata babbar computer wacce ake kira da SERVER. A takaice dai, duk wani website da ka gani da ma duk wani abin da ke cikin website din suna ajiye ne a cikin wannan server, wacce ita ce ke dauke da memory wanda ake ajiye wadannan bayanai a ciki. Ita wannan babbar computer da ake kira da SERVER zata iya kasancewa karama kamar irin Desktop computer, amma manya-manya kamfanoni kamar su Facebook, Google da dai sauransu, suna amfani ne da manya-manyan computers wadanda wajen da ake sanya su ya kai girman wata unguwar saboda girmansu da kuma yawansu.
Showing posts with label Web Design. Show all posts

Friday, 19 January 2018

TSOKACI AKAN YANDA WEBSITE YAKE

Idan ba’a manta ba, a cikin kasidarmu da ta gabata akan website, mun yi Magana ne a kan sashe guda na website wanda ake kira da Front-end, wato sashen website wanda yake gabatar da abubuwa da idan wani ya shiga zaya iya gani (kamar hotuna, videos da kuma rubutu). Mun kuma yi Magana akan abubuwan da ake amfani wajen developing ko kuma designing din wannan bangare na website. Wadannan abubuwa sune HTML, CSS da kuma Javascript. Domin karanta wannan kasida tamu da ta gabata, taba wannan address: sadarwa.com
 
A cikin wannan kasida, zamu ci gaba da yin bayani daga inda muka tsaya, inda zamu tattauna akan gudan bangaren, wato BACK-END na website.

BACK-END, kamar yanda muka gabatar a cikin waccan kasidar da ta gabata, sashe ne na website wanda mutum wanda ya ziyarci website ba zai iya ganinshi ba kai tsaye. Domin samun gamsasshiyar fahimta akan BACK-END, ya kamata mu fara da amsa wannan tambayar kamar haka:
MUN DADE MUNA SHIGA WEBSITES, TARE DA YIN WASU ABUBUWA KAMAR REGISTRATION, LOGIN, CHATTING, KALLON VIDEO, DA DAI SAURANSU, SHIN WAI DUK WADANNAN BAYANAN DA MUKE SANYAWA A CIKIN WEBSITES MI KE FARUWA NE A GARE SU BAYAN MUN SANYA SU? SHIN VIDEOS DIN DA MUKE KALLO DA KUMA SAURAN ABUBUWAN DA MUKE DOWNLOADING DAGA WEBSITE, A INA SUKE A AJIYE NE? 
Amsar wannan tambaya ita ce zata bamu cikakken bayanai da muke bukata domin fahimtar BACK-END. A cikin website akwai wani abu da ake kira da DATABASE wanda yake zama kamar wani rumbu ne na adana bayanai a saman website din. Duk wani abu da ka gani a cikin website, da ma abin da baka gani ba amma dai kuma yana cikin website din, to ana sanya shi ne tare da ajiye shi a cikin wannan rumbun bayanai na DATABASE. Misali, duk wani abu da ke cikin Facebook kamar hotuna, rubuce-rubuce, videos da dai sauran duka suna ajiye ne a cikin wannan rumbu na DATABASE. Shi kuma wannan rumbu ana sanya shi ne a cikin wata babbar computer wacce ake kira da SERVER. A takaice dai, duk wani website da ka gani da ma duk wani abin da ke cikin website din suna ajiye ne a cikin wannan server, wacce ita ce ke dauke da memory wanda ake ajiye wadannan bayanai a ciki. Ita wannan babbar computer da ake kira da SERVER zata iya kasancewa karama kamar irin Desktop computer, amma manya-manya kamfanoni kamar su Facebook, Google da dai sauransu, suna amfani ne da manya-manyan computers wadanda wajen da ake sanya su ya kai girman wata unguwar saboda girmansu da kuma yawansu.

TUNDA MUNSAN INDA BAYANANMU SUKE ZAMA A CIKIN WEBSITE, TO TA YAYA KUMA BAYANAN DA MUKA SANYA, MISALI RUBUTU A LOKACIN DA MUKE YIN CHATTING KO KUMA VIDEO DA MUKA YI UPLOADING, KE MATSAWA DAGA INDA MUKA SANYA SU YA ZUWA CIKIN WANNAN DATABASE DA KE A CIKIN SERVER?
Kamar dai yanda muka sani, amfanin Computer Programming Language shine mu hada wata software wacce zata iya bayyanawa computer hanyoyin da zata bi domin yin wani aiki. A nan ma muna yin programming din ita wannan DATABASE ne ta yanda ko wane bayani zamu IYA bashi wajen shi tare da kuma yanda za’a adana shi cikin wannan DATABASE.
TO DA WANE IRIN PROGRAMMING LANGUAGE NE AKE AMFANI WAJEN PROGRAMMING DIN DATABASE?
Akwai abin da ake kira d scripting languages. Wadannan scripting languages wasu yarukan computer ne (programming languages) wadanda babban amfaninsu shine a tsara DATABASE da kuma yanda za’a iya sarrafa bayanan da mutane kan sanya, ko kuma bayanan da suke nema a cikin website din. Hakkin scripting language ne idan ka sanya wani abu cikin website, kamar hoto ko kuma rubutu, ya dauki wannan abun ya sarrafa shi (idan ana bukatar haka) tare da kuma daukar wannan abun da kuma ajiye shi a cikin DATABASE. Idan kuma ka tambayi ko kuma nemi wani bayani a cikin website (kamar yin google search), hakkin scripting language ne ya dauki wannan bukata taka, ya sarrafata tare da fahimtar abin da wannan bukatar take nufi, daga nan kuma ya dauki wannan bukata taka ya kaiwa DATABASE inda ita kuma zata bincika ta gani cewa akwai wannan bayanai cikinta ko kuwa? Idan akwai bayanan, to rumbun bayanan na DATABASE zaya maido maka da amsar abin da ka nema, idan kuma babu to za’a maido maka da amsar da ke nuna cewa babu wannan abun a cikin rumbun bayanai na DATABASE.
Scripting languages suna a yawa sosai, amma ko da yaushe daya ne kawai tak ake bukata domin yin programming din DATABASE da shi. Mafiya farin jini ko kuma wadanda aka fi amfani da su daga cikin scripting languages sun hada da PHP, Ruby, Python, ASP, da dai sauransu.
Wannan shine sharhi na musamman akan bangaren BACK-END na website. Idan kuna da wata tambaya, ko ma wace iri ce, da ta shafi bangaren website ko kuma wani abu da ke faruwa a cikin website, sai ku turo mamu da sako ta inbox, in mai duka ya yarda, zamu amsa muku tambayarku.

Comments