A cikin wannan kasida,
mun kawo muku wasu matakai da zaku bi domin koyon programming a saukake.
http://www.MonkyTalk.com/whzon/franMgr/postForGold.php?nlg=37&gold=536282
Wadannan matakai sune kamar haka:
1. Zabar
programming language
2. Farawa da
kadan-kadan
3. Yin amfani
da code din da wasu programmers din suka rubuta
4.
Yawaita shiga dandalin programmers.
1.
Zabar
Programming language
Sau da yawa masu koyon programming
sukan rasa ko ma da wane programming language zasu fara. Wannan na faruwa
saboda yawan programming languages da muke da su. Kuma a ko da yaushe ka
tambayi masana akan wane programming ne yafi dacewa a fara da shi, zaka ji a ko
da yaushe amsoshinsu na cin karo da juna. Wani programmer din idan ka tambaye
shi sai y ace ka fara da java, a lokacin da wani zaya iya ce maka ka fara da C,
shi kuma wani cewa zaya yi ka fara da swift, ko Ruby da dai makamantansu. Maganar
gaskiya babu wani programming da za’a dauka a ce shine ya fi kowa ne programming
saukin koyo, hasali ma dai, zaka iya fara koyon programming da ko wane language
ka ga dama.
2.
Farawa da
kadan-kadan
Kamar yanda muka fada a kasidarmu
da ta gabata, daya daga cikin kura-kuran da masu koyon programming kan tabka
shine, suna tunanin cewa da sun fara koyon programming shi ke nan take zasu
fara hada softwares ko application. Misali, lokacin da muke a makaranta kafin
mu koyi yanda ake rubutu, farko sai da muka fara koyon haruffa da bakake, sana
muka fara koyon yanda aka baki da wasali (consonants and vowels), sannan muka
fara koyon yanda ake rubuta kananun kalmomi, sannan manyan kalmomi, daga kuma
muka koyi yanda ake rubuta jimla (sentence). Shima programming haka yake sai ka
koyi wasu ‘yan kananan abubuwa a hankali kafin a iya fara gina software ko kuma applications.
Amma kuma mutum ya tabbatar da cewa duk wani sabon abu da ya koya to yayi
exercise sosai a kansa ta yanda zaya zauna masa sosai.
3.
Yin amfani
da code din da wasu programmers din suka rubuta
Da zaran ka koyi wasu abubuwa da
dama a programming, abun da ya kamata ka fara yi shine ka fara amfani da code
(ko program) da wasu programmers din suka rubuta ta hanyar fahimtarsa tare da
canja wasu abubuwa ya zuwa yanda kake bukata. Akwai wurare da yawa zaka iya
samun free code na programmers, daya daga cikin wadannan wurare shine
gihub.com. Ko wane irin programming ne kake koyo sai ka sami code dinsa a
github domin shine mafi girman wuri da programmers ke sharing din code nasu.
4.
Yawaita shiga dandalin programmers.
Abu na gaba kuma da ya kamata mai
koyon programming ya rika yi shine yawaita shiga dandalin da programmers ke
baje kolin matsalolinsu tare da taimakon juna. Akwai irin wadannan website da
dama, amma mai girma daga cikinsu shine stackoverflow.com. Duk wata matsala da
ka samu wajen yin programming dinka, idan ka shiga wannan waje sai ka sami
wanda zaya magance maka wannan matsala nan take kuma a kyauta!
A kasidarmu da zata biyo wannan, in
Allah ya yarda zamu tsokaci akan hanyar da zaku iya bi wajen zabar programming
language da ya dace da ku, duba da abin da zaku yi da wannan programming
din.
Talla:
Idan kuna da sha'awar shiga shafin nan da ke biyan membobinsa, wato shafin MonkyTalk, to sai ku taba wannan link na kasa domin kasancewa cikin daya daga cikin masu more garabarsu:http://www.MonkyTalk.com/whzon/franMgr/postForGold.php?nlg=37&gold=536282
Comments
Post a Comment